Connect with us

Featured

EFCC Ta Ƙwato Sama da Naira Biliyan 853 a Cikin Shekara Ɗaya

Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta ce ta kwato sama da N364.5bn da kuma dala miliyan 326.5 daga hannun masu laifi tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024. Hukumar ta bayyana wannan nasara a matsayin abin tarihi, inda ta ce an cimma hakan ne ta hanyar sa ido kan kudaden tallafin gwamnati da dama, ciki har da shirin PL-CNG, NG-CARES, NACA Global Fund, SESET, rancen AMCON da kuma shirye-shiryen tallafin babban bankin ƙasa CBN, kamar tallafin COVID-19 da wasu lamuni na musamman.

A tsakanin wannan lokaci, EFCC ta ce ta karɓi koke-koke 15,724, inda ta gudanar da bincike kan 12,928 daga cikinsu. Haka kuma ta gurfanar da mutum 5,081 a kotu, an kuma yanke hukunci kan mutum 4,171, yayin da shari’o’i 2,348 ke ci gaba da gudana a kotuna.

Hukumar ta bayyana cewa waɗannan alkaluma ba wai kawai lambobi ba ne, illa kuwa sako ne mai ƙarfi ga masu aikata rashawa cewa ba za a lamunci ayyukansu ba.

Ta ce dukkan kwace-kwacen kudi da kuma hukuncin da aka samu an gudanar da su ne cikin bin doka da kulawar kotu, abin da ya ƙara karfafa gwiwar jama’a ga ayyukan hukumar. EFCC ta yi alfahari da wannan nasara a matsayin shaida ta tasirinta wajen kare tsarin kuɗi na Najeriya, wanda kuma ya tabbatar da matsayin ƙasar a matsayin jagora a nahiyar Afirka wajen yaƙar cin hanci da rashawa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet