Connect with us

Featured

Rashin Tsaro: An Rufe Sama Da Makarantu 180 a Arewacin Najeriya

Rahoton binciken jaridar Daily Trust ya gano cewa akalla makarantu fiye da 180 a jihohin Arewacin Najeriya aka rufe saboda hare-haren ’yan ta’adda da matsalar tsaro. Jihohin da abin ya fi shafa sun haɗa da Zamfara inda aka rufe makarantu (39), Katsina (52), Benue (55), Niger (30), Sokoto (6), da Kaduna, inda makarantu da dama suka koma sansanin ’yan gudun hijira ko ma gidajen jami’an tsaro. Wannan na faruwa ne a yankunan da tuni suka kasance kan gaba wajen yawan yara da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, lamarin da ya ƙara ta’azzara matsalar jahilci.

A Zamfara, makarantu da dama a kananan hukumomi kamar Anka, Tsafe, da Kaura Namoda sun dade a rufe, wasu ma an kwace su daga hannun dalibai an maida su wurin zama ga sojoji. A Sokoto kuma, makarantu irin su Federal Government Technical College Wurno da Government Girls’ Secondary School Rabah har yanzu suna a kulle, yayin da wasu makarantu a ƙauyuka suka zama mafaka ga ’yan gudun hijira. Haka a Katsina, rahotanni sun nuna an rufe makarantu da dama sakamakon garkuwa da ɗalibai, ciki har da abinda ya faru a Kankara a 2020.

Haka ma a jihar Niger, makarantu a yankunan Shiroro, Rafi, da Mariga sun durkushe, wasu an maida su sansanin sojoji. Malamai sun ce dalibai kan shafe makonni a gida duk lokacin da aka ji motsin ’yan ta’adda a kusa. A Kaduna da Kebbi, al’ummomi da dama sun gudu daga kauyukansu, suka bar makarantu a wofi, yayin da a Benue an ce fiye da makarantu 55 an mayar da su wurin zama ga ’yan gudun hijira bayan hare-haren makiyaya.

Masana da ƙwararru sun yi gargadin cewa tsawon lokacin da makarantun ƙauyuka ke rufe zai iya ƙara talauci da jahilci a yankin. UNICEF da masana tsaro sun ce dubban yara na fuskantar barazanar fadawa cikin aikata laifi, shiga ƙungiyoyin ta’addanci, yin karuwanci ko aurar da su da wuri. Sun bukaci gwamnati ta dauki matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya da kuma maido yara makaranta kafin a rasa gaba ɗaya wata al’umma mai ilimi.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet