Connect with us

Featured

Gwamna Yusuf Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar Ƙididdiga Ta Kano

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nada Dr. Suraj Sulaiman a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan Jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi 05 ga Oktoba, inda aka bayyana cewa nadin ya fara aiki nan take. Sabon nadin ya biyo bayan cikar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Associate Professor Aliyu Isa Aliyu, wanda aka ɗaga matsayinsa zuwa Kwamishinan Ma’aikatar Kiwo. An umarci a gudanar da bikin mika da karɓar aiki tsakanin Litinin zuwa Juma’ar wannan mako.

Dr. Suraj Sulaiman ƙwararren masani ne a fannin lissafi da bincike. Ya kammala digirin digirgir (PhD) a Jami’ar Teknoloji ta Malaysia (UTM) tsakanin 2015 da 2018, inda ya yi bincike kan “Sabuwar Hanyar Lissafin Projective Polynomial Resultant ta amfani da Dixon, Jouanolou da Jacobian Matrices.” Ya kuma samu digirin digirgir na biyu (MSc) a Jami’ar Yasar, Izmir, Turkey (2012–2014) da digirin farko (BSc) a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano (2006–2010). Haka kuma, ya fara tafiyar iliminsa da samun Diploma a fannin Mathematics Education a CAS Kano tsakanin 2004 zuwa 2006.

A sakonsa na taya murna, Gwamna Yusuf ya yaba da wannan nadin, yana mai bayyana Dr. Sulaiman a matsayin ƙwararren masani wanda zai kawo sabbin dabaru da inganta aikin Hukumar Kididdiga. Gwamnan ya nuna cikakken tabbacin cewa gogewarsa a fannin bincike da koyarwa za ta taimaka wajen inganta tsarin tattara bayanai da fitar da sahihan alkaluma a jihar.

Gwamna Yusuf ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na amfani da bayanan kididdiga wajen tsara manufofin gwamnati yadda ya kamata. Ya ce sahihan bayanai suna da matuƙar muhimmanci wajen ingantaccen tsari da gaskiya a harkokin gwamnati, bugu da ƙari da kuma tabbatar da cigaba mai ɗorewa a Kano.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet