Connect with us

Featured

Najeriya Za Ta Fara Haƙo Gangar Mai Miliyan 1.8 a Kullum – NNPCL

Shugaban Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL), Bayo Ojulari, ya bayyana cewa ana sa ran ƙasar za ta ƙara yawan haƙon ɗanyen mai zuwa gangan miliyan 1.8 a kowace rana kafin ƙarshen shekarar 2025. Ojulari ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi 05 ga Oktoba, yayin da yake sanar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu cigaban ayyukan kamfanin a jihar Legas, kamar yadda kafar Channels TV ta ruwaito.

Ojulari ya bayyana cewa gyare-gyaren da kamfanin ya gudanar a watannin Agusta da Satumba sun fara haifar da sakamako, tare da tabbatar da cewa za su taka muhimmiyar rawa wajen ƙara yawan fitar da mai daga watan Oktoba zuwa ƙarshen shekara. Ya ce kamfanin na aiki tuƙuru wajen ganin an cimma wannan buri da nufin ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.

A cewarsa, “Muna fatan kafin ƙarshen shekarar nan mu kai ga haƙo aƙalla gangan ɗanyen mai miliyan ɗaya da dubu 800 a kullum.” Wannan, a cewarsa, zai zama muhimmin ci gaba ga Najeriya a ɓangaren samar da mai da kuma tabbatar da matsayin ƙasar a kasuwar duniya.

A halin yanzu dai Najeriya na haƙo gangan miliyan 1.71 na ɗanyen mai a kullum, lamarin da ya sanya ta kasance cikin ƙasashen da ke kan gaba wajen samar da mai a ƙungiyar OPEC. Ƙarin samar da gangan mai zai taimaka wajen ƙara kuɗaɗen shiga da kuma inganta martabar Najeriya a kasuwar man duniya.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet