Connect with us

Featured

Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Jami’an Rigakafin Ƙyanda

Hukumomin lafiya a jihar Kano sun yi karin bayani kan dakatar da wasu jami’an lafiya a karamar hukumar Kabo, bisa zargin yin zagon kasa ga aikin rigakafin cutar ƙyanda. An ɗauki matakin ne yayin da jihar ke gudanar da gangamin rigakafi tare da sauran jihohin ƙasar, wanda ya shafi yara sabbin haihuwa har zuwa shekaru 15.

Gangamin yana da nufin kare yara daga manyan cututtuka kamar ƙyanda, sarke haƙora da mashaƙo, ta hanyar ba su allurar rigakafi kyauta a cibiyoyin lafiya da wuraren da aka tanada. Hukumar ta ce matakin dakatarwar ya zama dole ne domin tabbatar da cewa duk masu ruwa da tsaki sun gudanar da aikin cikin gaskiya da tsoron Allah.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an da aka dakatar suna daga cikin masu kula da aiwatar da rigakafi a yankin, kuma suna fuskantar bincike kan yadda suka gudanar da aikinsu. Haka kuma, wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki tare da gwamnati wajen gudanar da gangamin rigakafi sun shiga jerin wadanda ake bincika.

Hukumomin lafiya sun tabbatar da cewa za a ɗauki mataki mai tsauri kan duk wanda aka samu da hannu a aikata laifi, tare da jaddada aniyar gwamnati ta tabbatar da cewa ko da ɗaya daga cikin yara ba a bari ya rasa allurar rigakafi ba saboda sakaci ko rashin gaskiya.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet