Connect with us

Featured

Jonathan Zai Gana Da Tinubu Kan Shari’ar Nnamdi Kanu — Sowore

Mai rajin kare haƙƙin ɗan adam kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, ya bayyana cewa tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya amince da yin ganawa da Shugaba Bola Tinubu kan ci gaba da tsare shugaban Ƙungiyar ‘Yan asalin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu. Sowore ya bayyana haka ne a shafinsa na X ranar Juma’a 10 ga Oktoba, bayan ganawa da Jonathan a Abuja, inda ya ce sun tattauna ne kan gaggawa da muhimmancin warware batun Kanu.

Sowore ya bayyana cewa Jonathan ya fahimci muhimmancin magance matsalar tsarewar Kanu don tabbatar da zaman lafiya, adalci da warkar da ƙasar daga raunin siyasa. Ya ƙara da cewa tsohon shugaban ƙasar ya tabbatar masa da cewa zai gana da Tinubu “nan ba da jimawa ba” domin tattauna batun. Wannan mataki, a cewar Sowore, na da muhimmanci ganin yadda kira na ƙasa baki ɗaya ke ƙaruwa kan batun.

Shirin Jonathan na ganawa da shugaban ƙasa, ya sa ya zamo daga cikin jerin fitattun ‘yan Najeriya da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, lauya mai rajin kare haƙƙin ɗan adam Femi Falana (SAN), Sanata Shehu Sani da wasu fitattun mutane daga sassa daban-daban na ƙasar, waɗanda ke kira da a bi shari’ar Kanu cikin adalci. Kanu dai yana tsare tun daga 2021 bayan kama shi a ƙasar waje, inda kuma aka dawo da shi Najeriya, duk da cewa kotuna da dama sun bayar da umarnin belinsa ko sakin sa.

Sowore ya sake jaddada kiran sa na a saki Kanu, yana mai cewa ana tsare da shi ne saboda tsayawa kan batun nuna wariya da ƙungiyarsa ta jima tana korafi a kai. Ya kuma yi kira ga manyan shugabannin siyasa, al’adu da addini irin su Peter Obi, Chukwuma Soludo, Alex Otti, Hope Uzodinma, Oby Ezekwesili da shugaban Ohanaeze Ndigbo, John Mbata, da su haɗa ƙarfi wajen neman a saki Kanu.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet