Connect with us

Featured

Rundunar Ƴansandan Jihar Kano Ta Ceto Wasu Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta samu nasarar ceto mutane uku da aka sace a wasu ayyuka biyu da ta gudanar tsakanin jihohin Kano da Kaduna, a wani bangare na yaki da ayyukan laifi. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne tsakanin 7 zuwa 9 ga Oktoba, karkashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori.

A samamen farko da aka gudanar a ranar 7 ga Oktoba, jami’an rundunar masu yaki da garkuwa da mutane tare da tawagar sintiri ta Bebeji, sun kai farmaki a kauyen Saya-Saya na karamar hukumar Ikara, Jihar Kaduna, bayan samun sahihan bayanai daga wani matashi mai shekara 21 da ya tsere daga hannun masu garkuwa. A wajen, an ceto wani tsoho mai shekara 65, Musa Idris, yayin da masu laifin suka gudu, suka bar babur da igiya a baya.

Haka kuma, a wani lamari daban a ranar 9 ga Oktoba, rundunar ta gano wani matashi mai shekara 19, Ashiru Murtala, wanda aka sace a kauyen Beli na Rogo, Jihar Kano, tun ranar 5 ga Oktoba. Masu garkuwar sun gudu suka bar shi a gonar rake a Hunkuyi, Jihar Kaduna, inda jami’an ‘yan sanda suka ceto shi ba tare da ya samu wani lahani ba.

Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Bakori, ya umurci a ba waɗanda aka ceto kulawar gaggawa, tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da farautar masu laifin da suka tsere. Ya kuma yabawa jami’an da suka gudanar da aikin bisa ƙwarewa da jarumtaka, yana mai cewa “ba wurin ɓuyar masu laifi a Kano.”

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet