Connect with us

Featured

Ƙungiyar ASUU Za Ta Tsunduma Yajin Aikin Gargadi a Ranar Litinin

Ƙungiyar malaman jami’a ta ƙasa (ASUU) ta bayyana cewa za ta fara yajin aiki na gargadi na makonni biyu daga ranar Litinin 13 ga Oktoba mai zuwa. Wannan mataki ya biyo bayan cikar wa’adin makonni biyu da kungiyar ta bai wa Gwamnatin Tarayya domin ta cika mata bukatun da ta daɗe tana jira a warware su. Duk da wa’adin ya kare ranar Lahadi, gwamnati ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da matakin da kungiyar ke shirin ɗauka.

Yayin da tattaunawa ke gudana tsakanin bangarorin biyu domin kauce wa tsaikon karatu a jami’o’i, Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa gwamnati ta shiga matakin ƙarshe na tattaunawa da ASUU kan al’amuran albashi, tallafin jami’o’i da yarjejeniyar 2009. Ya ce an fitar da Biliyan 50bn domin biyan hakkokin ƙarin albashi, yayin da aka tanadi Naira Biliyan 150bn a kasafin kudin 2025 domin gyaran jami’o’i a matakai uku. Ya kara da cewa gwamnati ta biya bashin karin girma da wasu hakkoki, sannan sauran za a kammala biya nan da shekarar 2026.

Sai dai Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ya zargi Ma’aikatar Ilimi da jinkirta daukar mataki kan muhimman batutuwa da suka shafi malaman jami’a. Ya ce idan gwamnati ba ta kawo muhimmiyar amsa kafin karewar wa’adin ba, to za su shiga yajin aiki na gargadi. A cewarsa, “Idan gwamnati ta fitar da wani muhimmin abu cikin sa’o’i 48, za mu koma wajen mambobinmu domin tattaunawa.” Rahotanni daga jami’o’in tarayya da dama, ciki har da Jami’ar Jos, ABU Zaria da Jami’ar Abuja, sun tabbatar da cewa tuni su ka fara shirye-shiryen shiga yajin aiki.

Ministan Ilimi ya roki malaman da su nuna hakuri da kuma rungumar tattaunawa maimakon yajin aiki, yana mai cewa gwamnati ta nuna gaskiya da niyyar warware matsalolin a cikin shekaru biyu da suka wuce. Haka kuma, ya bayyana cewa karo na farko ne Lauyan Gwamnatin Tarayya da Ma’aikatar Shari’a suka shiga tattaunawar kai tsaye domin tabbatar da ingancin doka da aiwatar da yarjejeniyoyi yadda ya kamata. Duk da haka, ASUU ta nuna cewa ba za ta dakatar da matakin ta ba sai gwamnati ta tabbatar da daukar cikakken mataki kan bukatun da aka jima ana jira.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet