Connect with us

Featured

EFCC Ta Ƙwato Kimanin Naira Biliyan 500 Daga Hawan Shugaba Tinubu Zuwa Yanzu – Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Hukumar EFCC ta ƙwato kadarori da kudade da suka kai fiye da naira biliyan 500 cikin shekaru biyu na mulkin Shugaba Bola Tinubu. Ya bayyana haka ne a wajen taron ƙarfafa gwiwa na kwana uku ga alkalan ƙasa karo na bakwai, wanda EFCC tare da Cibiyar Shari’a ta Ƙasa suka shirya a Abuja, kamar yadda Channels TV ta ruwaito. Shettima ya ce manufar gwamnatin Tinubu ta ba wa hukumomin yaƙi da cin hanci cikakken ‘yanci ba tare da tsoma baki ba, ta taimaka wajen ƙarfafa yaƙi da cin hanci da inganta gaskiya da rikon amana.

Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu a wurin taron, ya bayyana cewa a cikin shekaru biyu, EFCC ta samu nasarar samun sama da hukunci 7,000 da kuma ƙwato kadarori fiye da naira biliyan 500. Ya ce an mayar da kudaden da aka ƙwato cikin tattalin arzikin ƙasa domin tallafawa shirye-shiryen raya ƙasa, ciki har da tsarin lamunin ɗalibai da tsarin bashi na masu amfani da kaya.

Ya ƙara da cewa gwamnati na aiki tare da bangaren shari’a domin inganta walwala da yanayin aiki na alkalan ƙasa. Ya ce an riga an inganta albashin alkalan, kuma gwamnati za ta ci gaba da tallafa musu da kayan aiki da walwala don tabbatar da gaskiya da adalci.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu ba ta kare kowa daga bincike ko shari’a ba, tare da jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin rassan gwamnati wajen murkushe cin hanci. Ya gargadi alkalan ƙasa da su gudanar da aikinsu da gaskiya da kishin ƙasa, yana mai cewa “cin hanci ba ya barin kowa — mu duka muna fuskantar illolinsa iri ɗaya.” Ya bukaci a haɗa kai domin gina ƙasa mai tsabta daga cin hanci.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet