Connect with us

Featured

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Baiwa Gwamnatin Tarayya Mako 4 Ta Kawo Ƙarshen Matsalolin Malaman Jami’a

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) tare da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) sun haɗa kai domin neman mafita ta dindindin ga matsalolin da ke haifar da rikice-rikicen karatu a jami’o’in ƙasar. NLC ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin mako hudu domin kammala tattaunawa da dukkan ƙungiyoyin ma’aikatan manyan makarantu, ciki har da ASUU, SSANU, COEASU da ASUP. Wannan mataki ya biyo bayan ganawar gaggawa da NLC ta gudanar da shugabannin ƙungiyoyin ilimi kan yadda za a kawo ƙarshen yajin aiki da ya tilasta rufe jami’o’i a fadin ƙasa.

Tun farko, ASUU ta fara yajin aiki bayan cikar wa’adin gargadin kwana 14 da ta bai wa gwamnati kan batutuwan da suka shafi albashi, alawus, da aiwatar da yarjejeniyar 2009. Duk da ikirarin Ministan Ilimi, Tunji Alausa, cewa gwamnati ta saki N50bn don biyan alawus da kuma ware N150bn a kasafin 2025, ASUU ta ce wadannan matakan ba su wadatar ba. Malaman suna bukatar cikakken aiwatar da yarjejeniyar, biyan albashin watanni uku da rabi da aka hana, da kuma samar da kudaden da za su tabbatar da dorewar jami’o’i.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa idan gwamnati ta kasa kammala tattaunawa cikin mako hudu, za su kira yajin aiki na ƙasa gaba ɗaya. Ya soki manufofin “ba aiki, ba albashi” na gwamnati, yana mai cewa daga yanzu za su ɗauki matsaya ta “ba biyan albashi, ba aiki”, domin mafi yawan yajin-aiki a ƙasar na faruwa ne saboda gwamnatin da ta saba alkawari.

Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ya jaddada goyon bayan ƙungiyarsa ga NLC, yana mai cewa ba za su sake halartar tattaunawa da wakilan gwamnati da ba su da ikon yanke hukunci ba. Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta daina raina ƙungiyoyin ilimi kuma ta ba bangaren ilimi muhimmancin da ya dace. A yanzu dai yajin aikin ASUU ya shiga rana ta takwas a yau Talata 21 ga Oktoba, 2025.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvmarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasibomcasibomjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasibomgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet