Featured
Batun Cewa Gwamnatin Tarayya Ta Karya Farashin Abinci Ba Gaskiya Bane – ADC
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta zargi gwamnatin tarayya da rashin gaskiya game da ikirarin da take yi cewa an samu karuwar samar da abinci a cikin gida. Jam’iyyar ta ce wannan batu ba gaskiya ba ne saboda matsalar tsaro da ta addabi manoma musamman a arewacin ƙasar, wanda hakan ya tilasta da dama daga cikinsu barin gonakinsu.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta bayyana cewa gwamnati tana boye abincin da aka shigo da shi daga ƙasashen waje yayin da miliyoyin ‘yan ƙasa ke fama da yunwa. Jam’iyyar ta ce wannan mataki wata hanya ce ta samun rinjaye na siyasa.
ADC ta kuma bayyana cewa raguwar farashin abinci da gwamnati ke ta ikirari ba shi da tushe, domin abin da ke faruwa shi ne kasuwanni sun cika da kayayyakin waje sakamakon waiver da gwamnati ta bayar ga ‘yan kasuwa. Ta ce hakan na cutar da manoma a cikin gida da ke fuskantar tsadar taki, tsaro mara kyau da karancin kayan noma.
Jam’iyyar ta yi kira da a sake duba tsarin noma gaba ɗaya domin kare rayuwar manoma, tabbatar da tsayayyen farashin abinci, da kuma samar da cikakkiyar manufar noma mai dorewa wadda za ta ba Najeriya ikon dogaro da kanta wajen samar da abinci.
