Featured
Kotu Ta Ci Tarar Direba Naira Miliyan 3 Sakamakon Tuƙin Ganganci
Kotun Babban Birnin Tarayya, Abuja, ta yanke wa wani direba mai suna Yusuf Baba hukuncin dauri na wata uku ko tara ta ₦50,000, tare da umartar shi da ya biya ₦3,190,000 a matsayin diyya saboda lalata motar sintirin FRSC da wasu motocin da aka kama yayin yunƙurin tserewa daga hannun jami’an hukumar.
Lamarin ya faru ne a ranar 10 ga Yuni, 2025, ƙarƙashin gadar Dantata, lokacin da jami’an FRSC suka dakatar da motar Baba saboda tukinsa da kaya fiye da kima yayin zaman kotun tafi-da-gidanka. Sai dai maimakon tsayawa, ya gudu cikin ganganci, ya rasa kulawa da motarsa, ya buge motar FRSC da wata mota ta wani mai laifi, sannan ya tsere. Daga baya jami’an hukumar suka kama shi a kusa da CITEC Road, inda aka gurfanar da shi bisa laifin tuki cikin haɗari da kuma kai hari ga jami’in FRSC.
Kotun ta same shi da laifin tuki cikin haɗari, ta yanke masa hukunci kamar yadda doka ta tanada, sai dai ta wanke shi daga zargin kai hari ga jami’in hukumar. Haka kuma, ta dakatar da lasisin tuƙinsa na tsawon wata uku, tare da umartar shi da ya biya kudin gyaran motocin da ya lalata.
Shugaban FRSC, Shehu Mohammed, ya yaba wa kotun bisa wannan hukunci, yana mai cewa wannan lamari ya nuna cewa lokacin yin ganganci da rashin biyayya a hanya ya wuce. Ya gargadi direbobi da su rika bin ƙa’idar hanya, su mutunta jami’an tsaro, domin FRSC ba za ta lamunci duk wanda ke barazana ga rayuka da dukiyar jama’a ba.
