Connect with us

Featured

Sojojin Amurka Sun Fara Shirye-shiryen Kai Hari Najeriya

Amurka ta fara tsara wasu shirye-shiryen yuwuwar kai hare-hare a Najeriya, bisa umarnin Shugaba Donald Trump, wanda ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gazawa wajen kare Kiristoci. Rahoton jaridar New York Times ya bayyana cewa rundunar AFRICOM ta gabatar da zaɓaɓɓun dabarun soji uku ga Ma’aikatar Tsaro, waɗanda suka haɗa da farmaki mai tsanani da matsakaici da kuma mai sauƙi.

Zaɓin farmaki mafi girma zai haɗa da tura jiragen yaki daga jirgin ruwa a Tekun Gulf na Guinea domin kai hare-hare a arewacin Najeriya, yayin da matsakaicin zaɓi zai ta’allaka ne kan harin jiragen drone irin su MQ-9 Reaper da Predator. Zaɓin mafi sauƙi kuma shi ne a yi haɗin guiwa da rundunar sojin Najeriya ta hanyar musayar bayanan sirri da tallafin kayan aiki wajen yaƙi da Boko Haram da ISWAP.

Sai dai masana tsaro a Amurka da Najeriya sun gargadi cewa irin waɗannan hare-hare ba za su magance rikicin Najeriya ba, duba da rikice-rikicen da suka shafi filaye, ‘yan bindiga da rikice-rikicen siyasa. Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin zaluntar Kiristoci, tana mai cewa Trump ya dogara da bayanan bogi. Haka kuma China ta nuna goyon baya ga Najeriya tare da sukar barazanar Amurka.

Wasu tsofaffin manyan hafsoshin soji na Amurka sun ce duk wani yunkurin kai farmaki zai iya tayar da rikici fiye da warware matsala, musamman ganin Amurka ba ta da sansanonin drone kusa da yankin bayan janyewa daga Jamhuriyar Nijar. Masana sun ce rikicin yankunan Arewa da Tsakiyar Najeriya ya fi kama da rikicin manoma da makiyaya da kuma ayyukan ta’addanci da ke cutar da Musulmai da Kiristoci baki ɗaya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet