Featured
Gwamnatin Zamfara Zata Ɗauki Sabbin Malamai 500
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da daukar sabbin malamai 500 domin karfafa bangaren ilimi a fadin jihar. Wannan na zuwa ne bayan kammala wani tsari na tantancewa da Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati ta Jihar ta gudanar, karkashin jagorancin Hon. Aliyu Mohammed Tutur.
A cewar tutar, bayanan mutum 11,708 ne suka nemi aikin ta hanyar shafin yanar gizo, inda 8,184 suka cika ka’idojin cancanta aka kuma tantance su. Daga cikinsu, 3,105 ne suka shiga jarabawar kwamfuta, kuma bisa tsarin maki, 1,033 suka kai matsayin shiga ganawar baki-da-baki. Daga karshe, malamai 500 aka zaba bisa cancanta, inganci da adalci, musamman a muhimman darussa kamar Turanci, Lissafi, Kimiyyar halitta da kwamfuta.
Hukumar ta ce an dauki matakai da dama don tabbatar da tsari na gaskiya, ciki har da bude shafin tantancewa na intanet, binciken takardu, jarabawar kwamfuta da kimanta kwarewar masu nema. Ma’aikatar Ilimi ta jinjinawa Gwamnan bisa jajircewarsa na farfado da ilimi da kuma cike gibi a bangaren malamai masu kwarewa a makarantun gwamnati.
An bayyana cewa za a rarraba sabbin malamai zuwa makarantun jiha, musamman a yankunan karkara da nesa, domin tabbatar da daidaito da saukin samun ilimi ga kowane yaro. Wannan mataki ya zama babban ginshiki na sabbin gyare-gyaren ilimi da gwamnatin Gwamna Lawal ke aiwatarwa domin dawo da martabar karatu a Zamfara.
