Featured
Gwamnatin Kwara Ta Rufe Makarantu Huɗu Sakamakon Ƙaruwar Matsalar Tsaro a Yankin
A sakamakon sabon tashin hankalin da ya kunno kai a yankin Kwara ta Kudu, Gwamnatin Jihar Kwara ta umarci rufe dukkan makarantu a kananan hukumomi hudu — Isin, Irepodun, Ifelodun da Ekiti — bayan mummunan harin da ’yan bindiga suka kai garin Eruku da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku da kuma sace sama da 35 a coci. Kungiyar Malaman Makaranta (NUT) ta tabbatar da umarnin rufe makarantu, inda ta ce an dauki matakin ne saboda sabbin barazanar tsaro da suka bayyana a yankin.
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq, wanda ya ziyarci Eruku bayan harin daren Talata, ya bayyana cewa ya fara tuntubar manyan hafsoshin tsaro don kafa sansanin sojoji (Forward Operating Base) da kuma sabon Mobile Police Squadron a yankin, domin shawo kan matsalar. Wannan na zuwa ne bayan korafe-korafen mazauna garin da suka yi zargin cewa jami’an tsaro, musamman ’yan sanda, sun kasa kawo dauki duk da kasancewarsu a kusa da wurin da aka kai harin.
A zantawar su da Kakaki24, matasa da dama sun yi zanga-zanga tare da toshe hanyar Ilorin–Kabba, suna zargin jami’an tsaro da sakaci da kuma hana su bin ’yan bindigan lokacin da suka yi yunkurin kare kansu. Wasu mazauna garin sun ce harin na zuwa ne bayan wata doguwar azaba da su ka sha fama da ita tsawon watanni, ciki har da garkuwa da manoma da mazauna gida-gida. Shugabannin addini kuma sun yi gargadin cewa harin da aka kai cikin coci yana iya haifar da fassarar cewa ana kai hari kan al’ummar Kirista a yankin.
Masarautar Eruku da hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa karin jami’ai, tare da motocin kariya, za su fara sintiri nan take, yayin da mazauna ke kira ga gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa kan iyakokin da ke da rauni, hanyoyin da ba sa wucewa, da karancin jami’an tsaro. Harin Eruku ya biyo bayan jerin tashe-tashen hankula da ake ci gaba da fuskanta a kan iyakar Kwara da Kogi da Ekiti, inda ake zargin ’yan bindiga suna komawa bayan sun tsere daga matsin lamba a wasu dazuzzukan makwabta.
