Connect with us

Featured

Sace Ɗaliban Kebbi Ya Nuna Gazawar Gwamnatin Tarayya – Atiku

A ranar Laraba 26 Nuwamba 2025, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya soki gwamnatin tarayya kan sakin daliban mata da aka sace a Jihar Kebbi, yana mai cewa ba abin murna ba ne, illa nuna tabarbarewar tsaro a Najeriya. Atiku ya ce ’yan ta’adda na gudanar da ayyukansu ba tare da tsangwama ba, yayin da gwamnati ke kokarin kare kanta da bayanai a kafafen yada labarai.

Atiku ya yi wannan martani ne bayan tattaunawar Bayo Onanuga, mai ba Shugaban Kasa shawara kan yada labarai, wanda ya bayyana cewa DSS da sojoji sun bi sawun masu garkuwa da mutane kuma suka tuntube su ba tare da biyan kudin fansa ba. Sai dai Atiku ya yi watsi da wannan bayani, yana tambayar dalilin da yasa ba a kama ko kakkabe wadanda suka yi garkuwar ba duk da ikirarin gwamnati na samun bayanan sirri. Ya kara da cewa gwamnati ba ta da hujjar yabawa kanta saboda tattaunawa da ’yan ta’adda maimakon dakile su.

Kakaki24 ta tattaro cewa Atiku ya ce wannan lamari ya nuna yadda ’yan bindiga ke zama tamkar “sabuwar gwamnati” suna karbar kudi, suna tattaunawa, sannan suna komawa jeji don sake sace wasu. Ya yi tir da yadda gwamnati ke bayyana lamarin a matsayin nasara, alhali hare-hare da garkuwa da mutane na cigaba da ruruwa a fadin kasa. Har ila yau, ya lura cewa gwamnatin tarayya ta bayyana farin ciki da sakin daliban, yayin da Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya ce babu kudin fansar da aka biya.

An sace dalibai 25 ne a ranar 17 ga Nuwamba daga makarantar Government Girls’ Secondary School da ke Maga, inda aka kashe ma’aikaci guda, sannan daya daga cikin daliban ta tsere, ta rage su 24 har zuwa sakin da aka yi a ranar Talata. Shugaba Tinubu ya bukaci karin jami’an tsaro a yankunan da ke fama da matsaloli, tare da umarni kan ci gaba da ceto sauran wadanda ke hannun ’yan bindiga a kasar.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet