Featured
Gaskiya Ta Fara Bayyana Akan Zarge-zargen Da Ake Yi Min – Abubakar Malami
Tsohon Ministan Shari’a na Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya ce ganawarsa da hukumar EFCC ta gudana lafiya bayan samun gayyata daga hukumar. Ya wallafa hakan ne a X (Twitter) da safiyar Asabar, 29 ga Nuwamba 2025, inda ya tabbatar da cewa an sake shi tare da tsara masa wani sabon zama don cigaba da bincike.
Kakaki24 ta tattaro cewa Malami ya ce gaskiya za ta fara bayyana kan zarge-zargen da ya kira “ƙirƙira” da ake masa. Ya jaddada cewa ya halarci gayyatar ba tare da jinkiri ba saboda bin doka da kuma manufarsa ta bayyana kai don nuna gaskiya da amana, tun daga lokacin da yake a kujerar mulki.
A baya dai EFCC ta gayyace shi kan zargin rashawa da ake cewa ta faru a lokacin da yake Minista a gwamnatin Buhari. Malami ya shaida wa al’umma cewa hadin kai da EFCC wani bangare ne na dabi’un shugabanci nagari da ya tsaya kai da fata kansu.
Ya roki ‘yan Najeriya su kasance cikin shiri da bibiyar abin da ke tafe, yana mai cewa zai rika sanar da su duk wani ci gaba da aka samu. Kakaki24 ta lura cewa shirin binciken zai ci gaba ne yayin da hukumar ke tabbatar da gaskiya da bin doka wajen gudanar da aikinta.
