Connect with us

Featured

Bauchi : Mata 3 Daga Cikin 10 Da Suke Da Juna-Biyu a Gida Suke Haihuwa – UNICEF

Gwamnatin Jihar Bauchi tare da UNICEF sun bayyana manyan gibin da ake samu a bangaren kula da lafiyar haihuwa, inda aka gano cewa mata uku daga cikin goma har yanzu na haihuwa a gida duk da haɗarurrukan da ke tattare da hakan. A yayin taron wayar da kai da aka gudanar na kwanaki biyu a Bauchi, UNICEF ta jaddada cewa makomar ƙasa na dogara ne ga yadda ake kula da matasa, tana kuma kira ga gwamnati ta tanadi kasafin kuɗi ta musamman don lafiyar jima’i da haihuwa ta matasa domin kauce wa durkushewar ci gaban ƙasa.

Jami’ar UNICEF, Dr Nazhat Rafique (ta bakin Oluseyi Olosunde), ta ce barazanar da matasa ke fuskanta – ciki har da ɗaukar ciki da wuri, haihuwa ba tare da kulawar likita ba, da ƙarancin samun ingantacciyar kiwon lafiya – na buƙatar gaggawar shiga tsakani daga gwamnati, abokan hulɗa da al’umma. Ta yaba wa kafafen yaɗa labarai bisa rawar da suke takawa wajen inganta fahimtar jama’a game da abinci mai gina jiki da kare haƙƙin yara, tana mai cewa haɗin gwiwa da manema labarai muhimmin mataki ne wajen canza dabi’u da inganta rayuwar matasa.

A nata bangaren, jami’ar Bauchi Primary Healthcare Board Amina Balali ta ce babbar matsalar da ake fuskanta ita ce rashin kasafin kuɗi na musamman don lafiyar matasa, tare da ƙarancin ma’aikatan lafiya, rashin cibiyoyin lafiya masu sauƙin kai wa matasa, da gibin ilimi ga ma’aikatan lafiya. Ta bayyana cewa kashi 25.3% na ‘yan mata masu shekaru 15–19 na shiga ciki a Bauchi, lamarin da ta ce yana nuna muhimmancin daukar matakan gaggawa domin inganta walwalar matasa, wadda ita ce ginshiƙin makomar ƙasa.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet