Featured
Ƙungiyar Yarbawa Ta Goyi Bayan Hare-haren Amurka a Najeriya
Ƙungiyar Alliance for Yoruba Democratic Movements (AYDM) ta nuna goyon bayanta ga hare-haren soji na haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka da aka kai a jihar Sokoto, tana mai bayyana su a matsayin mataki mai muhimmanci wajen yaƙar tsattsauran ra’ayi da ta’addanci da ke ƙara ƙamari a ƙasar.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, ƙungiyar ta gargadi gwamnonin Kudu maso Yamma da su ƙara shiri da taka-tsantsan, tana cewa ’yan ta’adda na iya ɗaukar fansa ta hanyar kai hare-hare a yankin, musamman Lagos da wasu muhimman cibiyoyin tattalin arziƙi da ke da alaƙa da Shugaban Ƙasa.
Sai dai AYDM ta jaddada cewa matakan soja kaɗai ba za su magance matsalar ba, inda ta bukaci sake fasalin ƙasa, raba iko da ba wa kabilu ’yancin cin gashin kansu. Haka kuma ta shawarci gwamnatin Tinubu da ta faɗaɗa haɗin gwiwar tsaro da ƙasashe kamar Rasha da Isra’ila domin raunana ƙarfin ’yan ta’adda tare da aiwatar da gyare-gyaren cikin gida.
