Featured
Zargin Da Gwamnan Bauchi Yayi Akan Hukumarmu Ba Gaskiya Bane – EFCC
Hukumar EFCC ta yi watsi da zargin Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, cewa ana amfani da hukumar wajen takura masa da wasu jami’an gwamnatinsa. EFCC ta bayyana zargin a matsayin marasa tushe, tana mai jaddada cewa tana aiki ne ba tare da tasirin siyasa ba.
A wata sanarwa da ta wallafa, EFCC ta ce ikirarin da ake cewa ana amfani da ita ta hannun wasu ‘yan siyasa, ciki har da Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike, ba gaskiya ba ne. Hukumar ta ce ita mai zaman kanta ce, kuma ba ta bin son rai ko adawa a aikinta.
EFCC ta ƙara da cewa abin zargi ne a danganta ayyukanta da tasirin wani ɗan siyasa, tana mai nuni da cewa Bala Mohammed yana fuskantar shari’ar kuɗi tun kafin ya zama gwamna. Ta bukaci gwamnan da ya mayar da hankali kan mulki, ya bar hukumar ta gudanar da aikinta na yaƙi da cin hanci.
