Featured
EFCC Za ta Kashe Naira Biliyan 3.2 Wajen Siyan Kayan Tsaftace Ofis a 2026
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ware kudin da ya haura ₦3.2 biliyan domin ayyukan tsaftace ofisoshi, feshin maganin kwari da kuma abinci a kasafin kudin shekarar 2026. Wannan ya fito ne daga cikin kasafin kudin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa Majalisar Tarayya a ranar 19 ga Disamba.
Takardun kasafin kudin sun nuna cewa EFCC ta ware ₦278.6 miliyan don tsafta da feshin magani, ₦722 miliyan don abinci da lemo, tare da ƙarin ₦1.02 biliyan don man motocci da ₦1.2 biliyan don janareto. Haka kuma, an ware makudan kudade don gyaran gine-gine, kayan aiki da kula da lafiyar ma’aikata.
Masana harkokin jama’a sun nuna damuwa kan irin wadannan kashe-kashe, suna cewa suna nuna almubazzaranci a tsarin kasafin gwamnati. Sun gargadi cewa yawan kudaden da ake kashewa kan abubuwan yau da kullum na iya rage tasirin kasafi ga rayuwar talakawa, tare da bai wa wasu damar karkatar da kudaden jama’a.
