Connect with us

Featured

Gwamnatin Kano Ta Ɗauki Nauyin Rayuwar Mutumin da Aka Kashe Masa Iyalinsa a Ɗorayi

Gwamnan Jihar Kano ya kai ziyara ta’aziyya a yau Laraba 21 ga Janairu zuwa gidan Malam Haruna da ke unguwar Dorayi, mutumin da aka kashe masa iyali mutum bakwai a wani mummunan lamari da ya girgiza al’umma. Gwamnan ya bayyana matuƙar alhini da juyayi, yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta yi shiru ba wajen tallafa wa wanda bala’in ya rutsa da shi.

A yayin ziyarar, gwamnan ya sanar da bai wa Malam Haruna kujerar aikin Hajji da kuma Umara, tare da yin alkawarin siya masa sabon gida domin ya bar gidan da lamarin ya faru. Ya ce an dauki wannan mataki ne domin rage masa radadi da kuma ba shi damar fara sabuwar rayuwa cikin kwanciyar hankali.

Haka kuma, gwamnan ya bayyana cewa za a yi wa Malam Haruna aure nan ba da jimawa ba, inda gwamnatin jihar za ta dauki nauyin kula da shi da sabuwar matar tasa gaba ɗaya. Ya ce wannan tallafi na daga cikin kudurin gwamnati na farfaɗo da rayuwar wanda iftila’i ya rutsa da shi.

Bugu da ƙari, gwamnan ya ce dan uwan Malam Haruna mai suna Umar, wanda ke taimaka masa wajen rage kewa, zai kasance tare da shi a dukkan tafiye-tafiyensa, inda gwamnati za ta dauki nauyin duk wata tafiya da za su yi tare.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet