Featured
Tinubu Zai Tafi Türkiye a Yau Litinin
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a yau Litinin, 26 ga Janairu, 2026, domin ziyarar aiki zuwa Jamhuriyar Türkiye, kamar yadda Mai Ba shi Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce ziyarar na da nufin ƙarfafa kyakkyawar alaƙa da ke tsakanin ƙasashen biyu tare da buɗe ƙarin fannoni na haɗin gwiwa a tsaro, ilimi, ci gaban zamantakewa, ƙirƙira da sufurin jiragen sama. Ziyarar kuma martani ce ga irin wadda Shugaban Türkiye, Recep Tayyip Erdogan, ya kai Najeriya a 2021.
A yayin ziyarar, za a yi tattaunawar siyasa da diflomasiyya kan harkokin kuɗi, sadarwa, kasuwanci da zuba jari, tare da sa hannu kan yarjejeniyoyi (MoU) a binciken kimiyya, makamashi, haɗin gwiwar fasaha, kafofin watsa labarai da tsaro. Haka kuma, za a shirya taron kasuwanci tsakanin ’yan kasuwa daga ƙasashen biyu, yayin da ake sa ran shugaban zai dawo gida bayan kammala ziyarar.
