Connect with us

Featured

Ƴansanda Sun Kama Wani Shahararren Ɗan Daba a Kano

Rundunar ƴansandan Jihar Kano ta kama wani shahararren dan daba, Auwalu Ali da aka fi sani da Auwalu Dan Daba, bisa zargin jagorantar ayyukan daba da kai hare-hare kan jama’a. An kama matashin mai shekara 26 ne a ranar 31 ga Janairu ta hannun jami’an sashen Dorayi, bisa sahihan bayanan sirri.

Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Abdullahi Kiyawa, ya ce ana zargin Ali da shirya da kuma jagorantar ƙungiyoyin daba da ke kai wa jama’a hari tare da yi musu fashi a wasu sassan Kano. Ya ce jami’an tsaro sun samu nasarar cafke shi ne bayan wani shiri na musamman da aka gudanar.

A wani lamari daban, ‘Yansandan sashen Sharada sun yi saurin daukar mataki bayan an kira su a kan wani fashi da ake zargin an kai, inda matasa suka ƙona wani mai kwacen waya da ake zargi bayan harin da ya kai wa wata mata. An garzaya da matar zuwa Asibitin Murtala Mohammed Specialist, inda wani dan sanda ya yi jarumta ta hanyar bayar da jini, wanda ya ceci rayuwarta.

Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da sadaukarwar ‘Yansandan, musamman aikin bayar da jini, tare da gode wa jama’a bisa hadin kai da goyon bayan da suke bai wa rundunar.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet