Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 135 Domin Shari’o’in Zaɓen 2027
Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 135.22 a cikin kasafin kuɗin 2026 domin kula da shari’o’in da suka shafi zaɓe da bayan zaɓe. An bayyana hakan ne a cikin rahoton kasafin kuɗi da aka gabatar a Majalisar Wakilai.
An sanya wannan kuɗi ne a karkashin “Service-Wide Votes”, wanda ke nufin asusun gwamnati na tsakiya da ake amfani da shi wajen biyan buƙatu daban-daban da ba a ɗaura wa wata ma’aikata kai tsaye ba. Hakan na nuna cewa gwamnati na sa ran ƙarin shari’o’i da suka shafi zaɓe a nan gaba.
Sai dai jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin farar hula sun nuna damuwa kan wannan ware kuɗi, suna cewa yana iya nuna rashin amincewa da sahihancin zaɓe mai zuwa. Sun kuma buƙaci a tabbatar da gaskiya da adalci domin rage yawan shari’o’in zaɓe a ƙasar.
