Featured
Kotu Ta Sake Ɗage Hukuncin Bayar da Belin El-Rufai Zuwa Mako Mai Zuwa
Babbar Kotun Jihar Kaduna ta sake ɗage yanke hukunci kan belin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, wanda Hukumar ICPC ke tuhuma da laifuka da suka haɗa da zamba da cin hanci. Tun farko an shirya yanke hukuncin ne a ranar 14 ga Afrilu, 2026.
Rahotanni sun ce an kawo El-Rufai kotu da misalin ƙarfe 9 na safe cikin motar Hilux, yayin da yake fuskantar tuhume-tuhume guda tara. Sai dai zaman kotun bai wuce mintuna 30 ba kafin a sanar da ɗage yanke hukuncin.
Lauyan wanda ake tuhuma, Ubong Akpan, ya bayyana cewa an ɗage shari’ar zuwa ranar 21 ga Afrilu, 2026 saboda rasuwar wani na kusa da alkalin kotun, Dariyus Khobo, wanda hakan ya hana shi shirya hukuncin a kan lokaci.
