Featured
Zaɓen 2027: ‘Yan Majalisa 17 Sun Fice Daga ADC Zuwa NDC
Mambobi 17 na majalisar wakilai sun fice daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) zuwa Nigeria Democratic Congress (NDC). An sanar da sauyin nasu ne a zaman majalisar a ranar Talata 05 ga Mayu, 2026.
‘Yan majalisar da suka sauya sheƙar sun haɗa da Yusuf Datti, Uchenna Okonkwo, Adamu Wakili, Thaddeus Attah, George Ozodinobi, Lilian Orogbu, Oluwaseyi Sowunmi, Peter Aniekwe, Mukhtar Zakari, George Oluwande, Munachim Umezuruike, Emeka Idu, Jesse Onuakalusi, Ifeanyi Uzokwe, Afam Ogene da Abdulhakeem Ado.
Wannan na zuwa ne bayan fitattun ‘yan siyasa kamar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso sun fice daga ADC zuwa NDC, yayin da Hon. Leke Abejide shi ma ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
