Featured
Kotu Ta Amince El-Rufai Ya Je Abuja Domin Duba Lafiyar Idonsa da Haƙori
Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna ta bai wa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, izinin zuwa Abuja domin neman maganin ido da hakora. Hukumar ICPC ta ce kotun ta amince da bukatar ne a ranar Laraba 06 Mayu, 2026.
Mai magana da yawun ICPC, Okor Odey, ya bayyana cewa lauyoyin El-Rufai sun roki kotu ta umurci hukumar ta ba shi damar zuwa asibitocin da yake bukata domin samun kulawar lafiya. Kotun ta umarci ICPC ta rika kai shi asibitocin Mile Dental Clinic da Skipper Eye-Q Hospital da ke Abuja karkashin tsauraran matakan tsaro.
ICPC dai ta gurfanar da El-Rufai a kotu kan zargin damfara da halasta kudaden haram. Tsohon gwamnan ya musanta zarge-zargen, yayin da kotu ta taba ba shi beli kan kudi Naira miliyan 200 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.
