Featured
EFCC Ta Cafke Tsohon Ministan Wutar Lantarki Saleh Mamman
Jami’an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta Economic and Financial Crimes Commission sun cafke tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman bayan ya shafe lokaci yana ɓuya duk da hukuncin da aka yanke masa.
Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ke gudana a hedikwatar hukumar. Ya ce an kama Mamman ne da misalin ƙarfe 3:30 na daren Talata a yankin Rigasa da ke jihar Kaduna.
Mamman dai na cikin waɗanda aka yankewa hukuncin ɗaurin shekaru 75 a gidan yari, sai dai ya ɓuya bayan yanke hukuncin. Hukumar EFCC ta ce za ta ci gaba da ɗaukar matakan doka a kansa, yayin da ake sa ran ƙarin bayanai kan lamarin.
