Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Shirin Ƙaƙaba Sabbin Haraji Kan Sadarwa Da Fetur
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata rahotannin da ke cewa tana shirin ƙara sabbin haraji kan harkokin sadarwa ta waya da man fetur, tana mai cewa bayanan da ake yaɗawa ba sa nuna ainihin manufofinta kan batun haraji.
Musantarwar ta biyo bayan wasu rahotanni da suka danganta da shawarwarin Asusun Lamuni na Duniya (IMF), wanda ya ba da shawarar a duba yiwuwar ƙarin harajin VAT kan wasu fannoni domin ƙara kuɗaɗen shiga da tallafa wa ci gaban tattalin arziki.
A wata sanarwa da ma’aikatar kuɗi ta fitar, ta ce shawarwarin IMF ba tilas ba ne ga Najeriya, domin duk wani sabon haraji sai an bi tanadin doka da amincewar majalisa. Kakaki24 ta ruwaito cewa gwamnatin ta jaddada cewa har yanzu an dakatar da VAT kan man fetur, kuma babu wani sabon haraji da ake shirin ƙaƙabawa a halin yanzu.
