Featured
Ka Tozarta Najeriya a Idon Duniya : Rarara Ya Caccaki Davido
Fitaccen mawaƙin siyasa a Najeriya, Dauda Adamu Kahutu Rarara, ya soki shahararren mawaƙin Afrobeats, David Adeleke, kan wani mataki da ya ɗauka a yayin bikin FIFA World Cup countdown concert. Rarara ya ce abin da Davido ya yi ya bata sunan Najeriya a idon duniya.
Rarara na martani ne ga bayyanar Davido a wani taro da ya sanya rigar da ke ɗauke da saƙon “Bring Them Home” tare da sunayen ɗalibai da malamai da aka sace a jihar Oyo. Rarara ya zargi mawaƙin da fito da matsalar tsaro ta cikin gida zuwa gaban duniya, yana mai cewa hakan na iya haifar da yin mummunar fahimta game da Najeriya.
Ya kuma yi zargin cewa an yi hakan ne domin cimma wata manufa ta siyasa da kuma sukar gwamnati mai ci. Kakaki24 ta ruwaito cewa Rarara ya gargadi masu ƙirƙirar ‘content’ su yi taka-tsantsan wajen magana kan al’amuran tsaro, yana mai cewa irin waɗannan batutuwa na buƙatar fahimta da kulawa ta musamman.
