Featured
Ƴan Majalisar Wakilai Sun Buƙaci Tinubu Ya Sauka Daga Mulki Matuƙar Ba Zai Iya Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro Ba
Ƙungiyar marasa rinjaye ta Majalisar Wakilai ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mayar da hankali kan magance matsalolin tsaro da tattalin arziki ko kuma ya hakura da mulki. Sun ce ƙasar na fuskantar tabarbarewar tsaro, talauci da rikice-rikicen siyasa yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
Shugaban marasa rinjaye a Majalisar, Fred Agbedi, ya bayyana cewa kashe-kashen da ake yi, sace-sacen mutane da ci gaba da tsare ɗalibai a wasu jihohi sun nuna gazawar gwamnati wajen kare rayuka. Ya ce dole ne gwamnati ta dakatar da harkokin siyasar 2027 tare da mayar da hankali wajen ceto ƙasar daga matsalolin da suka addabe ta.
A nasa bangaren, tsohon gwamnan soja na Jihar Kaduna, Kanal Abubakar Dangiwa Umar mai ritaya, ya bukaci Tinubu ya bai wa tsaro fifiko. Haka kuma, Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Kasa (NHRC) ta bayyana cewa mutane 390 aka kashe sannan 202 aka sace a watan Mayun 2026. Kakaki24 ta ruwaito cewa ‘yan majalisar sun kuma nemi a sake fasalin tsarin tsaron ƙasa sannan a gudanar da bincike kan mutuwar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya.
