Featured
Kwankwaso Ya Goyi Bayan Dokar Da Ta Haramta Sauya Sheƙa Daga NDC Bayan An Ci Zaɓe
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda zai yi takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar NDC, ya bayyana goyon bayansa ga sabuwar dokar jam’iyyar da ta haramta wa zaɓaɓɓun jami’anta sauya sheƙa bayan sun ci zaɓe.
Mai magana da yawun Kwankwasiyya, Habibu Saleh Mohammed, ya ce Kwankwaso na ganin dokar ta yi daidai da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, domin tana ƙarfafa biyayya ga jam’iyya tare da hana siyasar anfani da jam’iyya wajen samun mulki sannan a bar ta.
Ya ce wannan matsaya ta yi daidai da abin da Kwankwasiyya ta daɗe tana kira a kai, musamman bayan ƙalubalen da ƙungiyar ta fuskanta sakamakon sauya sheƙar wasu manyan mambobinta zuwa wasu jam’iyyu. Kakaki24 ta ruwaito cewa NDC ta ce an samar da dokar ne domin ƙarfafa ladabi, biyayya da haɗin kai a cikin jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.
