Featured
Atiku ya buƙaci EFCC ta janye ƙudurinta na rufe asusun gwamnatin Osun
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki matakin EFCC na rufe asusun rabon kuɗaɗen gwamnatin jihar Osun. Ya bayyana matakin a matsayin barazana ga dimokuraɗiyya, yana mai cewa akwai alamar tambaya ganin cewa an bijiro da matakin ne kwanaki 10 kafin zaɓen gwamnan jihar.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan hulɗa da jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce daskarar da asusun gwamnatin jihar na iya kawo cikas ga tafiyar da gwamnati, jinkirta biyan albashi da kuma shafar ayyukan jama’a. Ya ƙara da cewa duk wani bincike ya kamata a gudanar da shi bisa tanadin doka ba tare da haifar da zargin tsoma baki a siyasa ba.
Read Also : Tinubu ya yaba da ceto mutane 308 daga hannun ƴan bindiga a Kwara da Neja
Atiku ya kuma yi zargin cewa ana amfani da wasu hukumomin gwamnati wajen matsa lamba kan jihohin da ke ƙarƙashin jam’iyyun adawa. Ya ce hakan na rage amincewar jama’a da hukumomin gwamnati tare da raunana tsarin dimokuraɗiyya.
Ya buƙaci EFCC ta gaggauta janye matakin da ta ɗauka kan asusun gwamnatin Osun, yana mai cewa al’ummar jihar ne za su fi fuskantar illa. Sai dai EFCC ta ce matakin yana da alaƙa da binciken zargin karkatar da kimanin naira biliyan 11, bai kuma shafi zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ba.
