Featured
Tun da na zama gwamnan Kaduna ban karɓi bashin ko sisi ba – Uba Sani
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce gwamnatinsa ba ta karɓi wani sabon bashi ba tun bayan da ya hau mulki a shekarar 2023, duk da cewa tana ci gaba da biyan bashin da ta gada daga gwamnatocin baya.
Uba Sani ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Alhamis, yayin da yake amsa tambayoyi kan yadda gwamnatinsa ke kashe kuɗaɗe da kuma ƙarin kuɗaɗen shiga da jihar ke samu.
Gwamnan ya ce a halin yanzu Jihar Kaduna tana ware kimanin naira biliyan 6.7 a kowane wata domin biyan bashin da ta gada. Ya ce rashin karɓar sabon bashi ya samo asali ne daga taka-tsantsan da kuma kyakkyawan tsarin kula da kuɗaɗen gwamnati.
Uba Sani ya kuma ce gwamnatinsa ta samu nasarori a fannonin noma, ilimi, bunƙasa sana’o’i da tsaro. Sai dai Jihar Kaduna na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalolin tsaro, musamman hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane.
