Addini
Batun addini ne ke taka rawa a shari’ar El-Rufai – Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci
Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya, NSCIA, ta nuna damuwa kan abin da ta kira alamun nuna wariyar addini a shari’ar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.
A wata sanarwa da Sakataren Janar na majalisar, Farfesa Is-haq Oloyede, ya fitar, NSCIA ta ce ta daɗe tana ƙaurace wa yin tsokaci kan shari’ar, domin tana da yaƙinin cewa kotuna za su tabbatar da adalci.
Read Also : Zaɓen 2027: An Fara Gangamin Yaƙin Neman Zaben Gwamnoni Da ‘Yan Majalisun Jihohi a Najeriya
Sai dai majalisar ta ce abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun sa ta fara ganin alamun cewa wariyar addini na iya taka rawa a shari’ar. Biyo bayan kalaman Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, kan El-Rufai.
NSCIA ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ɓangaren shari’a su tabbatar da cewa ba a amfani da hukumomin gwamnati ko tsarin shari’a wajen aiwatar da wata manufa ta bangaranci a kan El-Rufai. Ta kuma bukaci jama’a su guji kalaman tunzura jama’a da ka iya shafar shari’ar.
