Connect with us

Featured

Babu dalilin da zai sa ɗan arewa yaƙi goyon bayan Tinubu a 2027 – Abdul’aziz Yari

Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC a 2027, Abdulaziz Yari, ya ce babu wani dalilin da zai sa yankin Arewa ya ƙi goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a ƙoƙarinsa na neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027.

Yari, wanda tsohon Gwamnan Zamfara ne, ya bayyana hakan ne a Legas lokacin da ya jagoranci mambobin kwamitin zuwa fadar Oba na Legas, Rilwan Akiolu, domin tattaunawa kan shirye-shiryen zaɓen 2027. Ya ce ya kamata Arewa ta rama goyon bayan da Tinubu ya bai wa marigayi Shugaba Muhammadu Buhari a zaɓukan baya.

Read Also : Ba da yawun mu malaman jami’o’i a Arewacin Najeriya suka goyi bayan Tinubu ba – ASUU

Sanatan Zamfara ta Yamma ya ce Tinubu ya ƙi amincewa da matsin lambar da aka yi masa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2019 domin ya ba Arewa damar kammala wa’adin mulki. Yari ya ce bisa hakan, ya kamata mutanen Arewa su nuna godiya ta hanyar goyon bayan Tinubu a 2027, musamman bisa abubuwan da ya bayyana a matsayin ayyukan gwamnatin shugaban.

Yari ya ƙara da cewa goyon bayan da kwamitin yakin neman zaɓen ke bai wa Tinubu bai ta’allaka kawai da tsarin rabon mulki tsakanin Arewa da Kudu ba. Ya ce suna goyon bayansa ne saboda sun yi imanin ’yan Najeriya na son ya ci gaba da jagorantar ƙasar tare da aiwatar da manufofin gwamnatinsa.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet