Featured
Gwamnatin Neja ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Minna
Hukumomi a jihar Neja sun ƙaƙaba dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a Minna, babban birnin jihar, sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke a birnin.
Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan yaɗa labarai, Zayyanu A. Salihu, ne ya wallafa sanarwar a shafinsa na Instagram, inda ya ce dokar za ta fara aiki bayan Sallar Juma’a. Hukumomin sun shawarci jama’a da su mutunta dokar.
Read Also : Mutuwar Matasa a Neja: Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shugaban NSCDC na Jihar
Wani mazaunin Unguwar Tunga Sabon Titi, inda lamarin ya faru, ya shaida wa BBC cewa fusatattun matasa sun yi ta jefe-jefe, yayin da ƴansanda ke harbi. Ya ce ƴansanda sun harbi mutane huɗu, inda ɗaya daga cikinsu ya mutu nan take.
Da farko, jami’ai sun yi zargin cewa wata cuta ce ta yi sanadin mutuwar wasu matasan da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba. Gwamnatin jihar ta kafa kwamitin bincike, yayin da Gwamna Mohammed Umar Bago ya ayyana makoki na kwanaki uku tare da dakatar da yaƙin neman zaɓensa.

Pingback: Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin hukunta duk wanda aka samu da hannu a mutuwar matasa 37 a Neja - KAKAKI 24