Featured
Ina cikin ƙoshin lafiya kuma a shirye nake na cigaba da aiki gadan-gadan – Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya ce yana cikin ƙoshin lafiya, kuma a shirye yake ya koma bakin aiki, bayan kammala hutun aiki da yayi na tsawon wata ɗaya a Turai.
Tinubu ya bayyana hakan ne, jim kaɗan bayan isarsa filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas, inda ya yi watsi da jita-jitar cewa yana fama da rashin lafiya.
Read Also : Mutane 3 sun mutu, da dama sun jikkata yayin turmutsitsin jama’a a Gidan Gwamnatin Neja
Manyan jami’an gwamnati ne suka tarbe shi, ciki har da Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Femi Gbajabiamila, da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas.

Pingback: Sarkin Kano ya yi Alla-wadai da lalata fastocin Gwamnan Kano, tare da umartar gaggauta gyara su - KAKAKI 24