Connect with us

Featured

Zaɓen 2027: Jam’iyyun adawa na duba yiwuwar tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya

Shugabannin wasu jam’iyyun adawa sun ƙara kaimi wajen ƙoƙarin ganin sun samar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya, domin fuskantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027. A wani ɓangare na shawarwarin, shugabannin jam’iyyun sun gana da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar ADC, Atiku Abubakar, a Abuja.

Jam’iyyun da suka samu wakilci a ganawar sun haɗa da APM, PRP, wani ɓangare na PDP ƙarƙashin Kabiru Tanimu Turaki da SDP. Wata majiya ta ce shugabannin sun tattauna abubuwan da ake buƙata domin samar da ɗan takara guda, tare da shirin ganawa da sauran ‘yan takarar shugaban ƙasa.

Read Also : Yankari Game Reserve: A Forest Where Wild Animals and Humans Relate

PRP ce ta tabbatar da ganawar, inda Sakataren Yada Labaranta na Ƙasa, Muhammed Ishaq, ya ce Atiku ya karɓi ƙungiyar adawar tare da ƙarfafa gwiwar shugabannin da su ci gaba da haɗa kai. Jam’iyyar ta kuma ce ana shirin gudanar da wasu ganawa da shugabannin jam’iyyu da ‘yan takarar shugaban ƙasa.

Wannan yunƙuri ya biyo bayan shirin ƙungiyar G-100, wadda ke ƙoƙarin haɗa ADC, PDP, NDC, PRP, SDP da APM domin tattauna yiwuwar samar da ɗan takarar bai ɗaya. Sai dai har yanzu akwai tambayar ko ‘yan takarar daban-daban da magoya bayansu za su amince su janye domin mara wa ɗan takarar da za a cimma matsaya a kansa baya.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet