Featured
Ba za mu amince a yi mana maguɗi a zaɓen 2027 ba – David Mark
Shugaban Jam’iyyar ADC na ƙasa, Sanata David Mark, ya ce jam’iyyar ba za ta amince a yi mata maguɗi a zaɓukan 2027 ba. Mark ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin da tawagar Savannah Centre for Diplomacy, Democracy and Development ta kai ziyara hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin tsohon Alƙalin Alƙalan Najeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, ta ce ziyarar wani ɓangare ne na tattaunawar da cibiyar ke yi da jam’iyyun siyasa da shugabanninsu gabanin babban zaɓen 2027.
Read Also : Wasu daga cikin manufofin gwamnatin Tinubu sun jefa ƴan Najeriya cikin mawuyacin hali – Daniel Bwala
Ariwoola ya ce cibiyar na ƙoƙarin ganin an gudanar da zaɓe cikin ’yanci, gaskiya da adalci. Ya kuma buƙaci shugabannin ADC su tabbatar da cewa ’yan takararsu suna bin dokokin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), tare da kauce wa duk wani nau’in tashin hankali.
A nasa martanin, David Mark ya ce ADC za ta bi dokokin zaɓe tare da gudanar da harkokinta yadda ya dace, domin ƙara samun amincewar jama’a da tsarin dimokuraɗiyya.

Pingback: Dangote Cement Obajana Awards Scholarships, Empowers Farmers, Market Women At Jakura Community - KAKAKI 24