Connect with us

Featured

Al’ummar Kano Atiku Za Su Zaɓa

Daga Adnan Mukhtar

Akwai wani abu da mutane da dama daga wajen Kano ba su fahimta ba game da siyasar Kano. Siyasar Kano ba kamar ta sauran jihohin Najeriya ba ce. Za ka iya fahimtar hakan tun daga zamanin NEPU, lokacin gwagwarmayar neman ’yancin kai, Jamhuriyya ta Farko da ta Biyu, har zuwa dawowar dimokuraɗiyya a shekarar 1999.

Siyasar Kano siyasa ce da tasirin uban gida yake da matuƙar muhimmanci. Idan ka duba tarihin gwamnoni da Kano ta yi, za ka ga cewa kowannensu ya samu goyon bayan wani uban gida da ya taka muhimmiyar rawa wajen hawansa mulki. Misali, Alhaji Abubakar Rimi, Sabo Bakin Zuwo, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf. A cikin waɗannan shugabanni da na lissafa, ka faɗa min wanda uban gidansa bai taka muhimmiyar rawa wajen nasarar zaɓensa ba, musamman a zaɓen fidda gwani da kuma babban zaɓe.

Idan ba ka gudanar da bincike kan ra’ayin masu zaɓe ba, ba za ka iya tantance wanda zai lashe zaɓe da tabbaci ba. Amma za ka iya fahimtar wanda yake kusa da nasara, wataƙila saboda irin tallar da ake yi wa ɗan takara ko kuma farfagandar da ake yaɗawa a kansa.

A zamanin Jamhuriyya ta Uku, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya na jam’iyyar NRC ya lashe zaɓe ne bayan wasu jagororin SDP, ciki har da Alhaji Abubakar Rimi, suka sauya matsayinsu, suka marawa Gaya baya, tare da juya wa ɗan takararsu, Injiniya Magaji Abdullahi, baya. Wannan ya nuna yadda sauyin matsayar manyan jagororin siyasa zai iya shafar sakamakon zaɓe a Kano.

Abin da ya sa wasu suke ganin kamar Atiku Abubakar ba shi da tasiri sosai a siyasar Kano shi ne rashin samun goyon bayan wasu tsofaffin gwamnoni da sanatoci daga jihar. Irin waɗannan mutane suna da tasiri a siyasa, kuma suna iya taka muhimmiyar rawa wajen fito da ɗan takara da kuma taimaka masa wajen samun nasara.

Read Also : Ba dan Tinubu ba, da tuni tattalin arzikin Najeriya ya durƙushe — Shettima

Amma a nawa binciken, ba don ina goyon bayan Atiku ba, na fahimci cewa babu ɗan takarar shugaban ƙasa da al’ummar Kano suke so a halin yanzu kamar Atiku Abubakar.

Ina tattaunawa da ’yan siyasa daga jam’iyyar APC, har da wasu shugabannin mazabu, kuma abin da nake yawan ji daga gare su shi ne yadda jama’a suke shan wahala a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu. Wannan shi ne ɗaya daga cikin dalilan da suke ganin zai sa su marawa Atiku baya.

Akwai bambanci tsakanin ɗan siyasa da talakan da ke zaɓe. Wani ɗan siyasa na iya ƙin ka, amma hakan ba yana nufin mutanen gari ma sun ƙi ka ba. ’Yan siyasa su ne suke neman jama’a da tallata ’yan takara, amma a ƙarshe, masu zaɓe ne suke yanke hukunci ta hanyar ƙuri’unsu.

Abin da Atiku yake buƙata a Kano shi ne yadda zai kare ƙuri’un da zai samu, domin a nawa hangen nesa, akwai gagarumin goyon baya da yake da shi a tsakanin al’ummar jihar.

Masu zaɓe a Kano, idan aka cire son zuciya da siyasar ƙiyayya, sun san wanda suke so. A ganina, Atiku Abubakar ne zaɓin al’ummar Kano, musamman idan aka yi la’akari da tsadar rayuwa da kuma wahalhalun da jama’a suke fuskanta a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

A siyasar Kano, kada a raina ra’ayin talaka. Domin a ƙarshe, ba yawan manyan ’yan siyasar da ke tare da ɗan takara ne kaɗai ke tabbatar da nasara ba; ƙuri’ar talaka ce ke yanke hukunci.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet