Featured
Ƴan adawa ne suka jefa Najeriya cikin yunwa da talauci – Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya zargi ‘yan adawa da gwamnatocin da suka gabata da haddasa yunwa da talauci da ‘yan Najeriya ke fuskanta, yana mai cewa gwamnatinsa na kokarin gyara matsalolin tattalin arzikin ƙasar.
Tinubu ya bayyana hakan ranar Asabar a Kaduna yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, inda ya nemi ‘yan Najeriya su sake zaɓarsa a zaɓen shugaban ƙasa na Janairun 2027 domin ci gaba da manufofin farfaɗo da tattalin arziki.
Read Also : Ba don Tinubu ba, da Buhari bai zama shugaban Najeriya ba – Shettima
Ya kuma kare matakin cire tallafin man fetur, yana mai cewa hakan ya zama dole domin dakile cin hanci da rashawa da kuma asarar kuɗaɗen gwamnati. Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen inganta rayuwar matasa.
Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya bukaci mazauna jihar su sake zaɓar Tinubu, yana mai cewa gwamnatin tarayya ta tallafa wajen ayyukan more rayuwa, ilimi, lafiya, noma da tsaro. Ya ce an ware Naira biliyan 178 domin gyaran hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Pingback: An fitar da matar da ta shigo da Ebola Najeriya zuwa Switzerland - KAKAKI 24