Featured
Za a kammala shirin kafa ƴansanda jihohi kafin karshen Disamba 2026 – Majalisar Dattawa
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawan Najeriya, Opeyemi Bamidele, ya ce ana sa ran kammala shirin kafa ƴansandan jihohi kafin ko a cikin watan Disamban 2026.
Bamidele, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan yi wa Kundin Tsarin Mulki na 1999 gyaran fuska, ya bayyana haka ranar Alhamis, yana mai jaddada muhimmancin wannan ci gaba.
Read Also : Har yanzu INEC ba ta tabbatar da takarar Gwarzo ba
Ya ce amincewar majalisun dokokin kusan jihohi 30 ta cika sharadin samun goyon bayan kashi biyu bisa uku na jihohin ƙasar, kamar yadda Sashe na 9(2) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ya tanada.
Ya bayyana cewa abin da ya rage yanzu shi ne tattara rahotannin majalisun jihohin a hukumance, sannan majalisun biyu su amince da ƙudirin kafin a miƙa shi ga Shugaban Ƙasa domin sanya hannu. Ana sa ran kammala tsarin kafin ko zuwa Disamban 2026.
