Addini
Na ƙalubalanci Tinubu ya zo mu yi gasar karatun Al-Qur’ani – Dino Melaye
Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya kalubalanci Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya zo su yi gasar karatun Alƙur’ani, biyo bayan ziyarar shugaban zuwa Saudiyya domin gudanar da Umrah.
Melaye ya yi wannan kalubale ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, 02 ga Nuwamba 2026, inda ya ce a shirye yake ya fafata da Tinubu a gasar kawo nassoshin Alƙur’ani idan shugaban ya dawo daga Saudiyya.
Read Also : Nagode wa hukumomin Saudiyya da suka bani damar shiga Ka’aba – Tinubu
A cikin sakon, Melaye ya ce: “Yanzu da Alhaji Bola Tinubu yake Umrah, da zarar ya dawo, ina kalubalantarsa zuwa gasar kawo nassoshin Alƙur’ani da ni. Babu wanda zai yi wa Allah wayo.”
Kalubalen ya zo ne bayan mai bai wa Tinubu shawara kan yada labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya wallafa bayanai kan irin ayyukan ibadar da shugaban yake yi a Saudiyya, ciki har da ziyararsa zuwa cikin Ka’abah mai alfarma a Makka.

Pingback: Tinubu ya taya Sarkin Musulmi murnar cika shekaru 20 kan karagar mulki - KAKAKI 24