Ilimi
Wasu cikin malamai sun sauke Shiek Ibrahim Khalil daga muƙaminsa

Wasu daga cikin Malaman jihar Kano sun sanar da sauke Shugaban Majalisar Malamai na jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil daga jagorancin majalisar bisa wasu laufuka da suke tuhumarsa da su.
Malaman sun bayyana hakan ne ta cikin wata takarda da suka fitar bayan taron manema labarai da suka yi.
Sanarwar wadda Ustaz Saifullahi Adam Assudani da Sheikh Khalifa Gama da sheikh Abdulkadir Ramadan da Kuma Imam Jamil Abubakar suka Sanya wa Hannu ta ruwaito cewa malaman sun ɗauki matakin ne da yawun dukkanin Malaman jihar Kano.
Haka kuma ta cikin sanarwar malamin sun zargi Shiek Ibrahim Khalil da ya gazawawajen ciyar da Majalisar malaman gaba.
Haka kuma sun ƙara da cewa majalisar ba ta yin aikin da aka dora mata na yin fatawa ga al’umma akan sababbin matsalolin da suke bijirowa a yanzu.
Malaman sun kuma zarge shi da Suka ce riƙa yin amfani da ofishin majalisar wajen yin taruka na ƙashin kansa.