Labarai
Kaduna: Sojoji sun kashe ƴan bindiga 40 a dajin Birnin Gwari

Shalkwatar tsaron Nijeriya ta ce, jiragen yaƙi sun yi nasarar hallaka ƴan bindiga 40 a wani luguden bama-bamai da suka yi musu a cikin dajin Kwaga da ke yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna.
BBC ta ruwaito cewa shalƙwatar ta ƙara da cewa, yayin hare-haren wanda sojojin suka kai ta sama sun lalata maɓoya da sansanonin ƴan ta’addar da dama a jihohin Kaduna da Katsina da kuma jihar Sokoto.
Haka kuma dakarun sun cafke wasu gawurtattun ƴan fashin daji da suka jima sun cim karensu ba babbaka a dajin Ɗan-gulbi na jihar Zamfara.
Haka kuma ta ruwaito cewa cikin ƴan fashin da aka cafke da masu kai musu bayanai da ke waɗanda ke cikin jerin mutanen da jami’an tsaro ke nema da suka haɗar da Mamuda Aliyu Dangulbi, da Rilwan Sani Dangulbi, da Yusuf Adamu Dangulbi, da kuma Yakubu Umar Maihaja, dukkansu a yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.