Tsaro
Neja: Ƴan bindiga sun buƙaci miliyan 60 na fansar mutanen da suka sace a masallaci

Rahotonni daga jihar Neja na cewa, ƴan bindigar nan da suka sace mutane 10 tare da kashi wasu da dama a ƙauyen Maza-Kuka da ke jihar Neja sun nemi naira miliyan sittin a matsayin kuɗin fansar mutanen.
A ranar Litinin ɗin makon nan ne ƴan bindigar suka kai farmakin wani masallaci lokacin da ake tsaka da gudanar da sallar Asubahi.
Rahotanni sun ce, ƴan bindigar a yayin harin sun hallaka mutane 18 tare da tafiya da wasu.
Sai dai BBC ta ruwaito cewa, jami’an ƴan sanda sun yi hasashen cewa harin na ramuwar gayya ne.