Ilimi
Da ɗumi-ɗumi: Hukumar NECO ta saki sakamakon jarrabawar ta bana

Hukumar shirya jarabawar kammala makarantun sakandare ta Najeriya NECO, ta saki sakamkon jarrabawar wadda ɗalibai suka rubuta a bana.
Shugaban hukumar Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ne ya sanar da sakin sakamakon a ganawarsa da manema labarai da yammacin yau Juma’a a shalkwatar hukumar da ke Minna babban birnin jihar Neja.
Ya ce, ɗalibai 1,226,796 ne suka rubuta jarrabawar cikin 1,233,631 da suka yi rijista.
Haka kuma ya ƙara da cewa, waɗanda suka zauna jarrabawar sun haɗar da ɗalibai maza 657,389 ne watau kaso 53.28, sai kuma mata 576,242 su kuma kaso 46.71.
Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ya kuma ce, ɗalibai 878, 925 ne suka ci darrusa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi, kenan an samu raguwa akan na bara.
Ya ƙara da cewa hukumar ta samu laifukan satar amsa guda 20,003, amma ya ragu idan aka kwatanta shi da na bara.