Labarai
Tsaro: Masarautar Ƙaraye ta yi Allah wadai ga masu yaɗa labaran ƙarya

Majalisar masrautar Ƙaraye da ke jihar Kano, ta yi tir da Allah wadai da wani labari da ake yaɗawa a kafar sada zumunta ta WhatsApp, cewar wai ƴan ta’adda daga jihohin Katsina da Zamfara sun yi sansani a wuraren da ake haƙar Mu’adinan ƙarƙashin ƙasa ba bisa ƙa’ida ba a wasu gundumomi uku da ke ƙarƙashin masarautar.
Hakan na cikin wata sanarwa da Jami’in yaɗa labarai na majalisar masarautar Haruna Gunduwawa, ya fitar da yammacin yau Talata.
Sanarwar ta ce, Wannan batu ƙarya ce kawai da aka kitsa ta da nufin cusa tsoro, zulumi da zaman ɗar-ɗar a zukatan al’umma domin cimma wani buri.
Haka kuma sanarwar ta ce, Lokacin da wannan munmunan labari ya kai ga kunnuwan Mai Martaba Sarki, ya tuntuɓi haɗakar jami’an tsaro da ke kai kawo domin daƙile ayyukan ta’addaci a masarautar da kuma Hakimansa waɗanda suka tabbatar da cewar wannan labari ƙarya ce tsagwaronta.
Masarautar ta Ƙaraye ta yi kira ga al’ummar masarautar da na jihar Kano baki ɗaya da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da gudanar da hakokinsu kamar yadda suka saba.
Sanarwar ta kuma ce, Gwamnati na yin matuƙar ƙoƙari na ganin ta kawar da dukkanin miyagun ayyuka a Najeriya baki ɗaya.
Masarauta ta buƙaci mutane da su cigaba da bada gudunmawarsu ta hanyar cigaba da yin addu’o’in samun cikakken zaman lafiya.